Kungiyoyin Gwagwarmayar Falastinawa Sun Dora Alhakin Abin Da Ke Faruwa A Kan Gwamnatin Isra’ila.
Kungiyoyin Falasdinawan sun taya shi murnar harin neman shahadar da aka kai a daren jiya a gabashin Tel Aviv, inda suka bayyana hakan a matsayin wani bangare na bacin ran al’ummar Palastinu na kare Masallacin Al-Aqsa.
Rahoton tashar Falasdinu Al-Youm, kungiyar Islamic Jihad ta sanar da cewa: Tozarta masallacin Al-Aqsa da sojojin gwamnatin mamaya da gungun ‘yan ta’addar sahyoniyawan yahudawa suka yi na nufin shelanta yaki kan al’ummar Palastinu da kuma tsallaka jan layi, don haka al’ummar Palastinu za su yi aiki tare wajen tunkarar gwamnatin mamaya da ta’addanci ta Isra’ila.
Har ila yau kungiyar ta Islamic Jihad ta kira wannan farmakin a matsayin nasara ga masallacin Al-Aqsa.
Wasu Palasdinawa biyu ne dai suka kai hari a yankin Al-Aad da ke gabashin birnin Tel Aviv wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu ‘yan sahayoniya 4 ‘yan share wuri zauna, tare da jikkata wasu uku na daban.
Garin Al-Aad yana kudu da Ras al-Ain da kuma garin Majdal al-Sadiq da aka yi watsi da shi, mai tazarar kilomita 25 gabas da Tel Aviv, kusa da gabar yamma da kogin Jordan da kuma garin Deir Oak.
Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qasim a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa, farmakin na daga cikin abin da ke nuan fushin al’ummar Palastinu kan wuce gona da irin Isra’ila a Falasdinu, yana mai jaddada cewa harin da aka kai kan masallacin Al-Aqsa ba zai yiwu ya wuce ba tare da martani ba.