Kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta bayyana cewa, matsayin isra’ila na mai sa ido a taro karo na 55 na dakatacce ne kuma ba’a gayyaci isra’ilan a taron da aka gudanar ba, hakan ta sa aka fitar da wakilin isra’lan daga wajen taron.
Shugaban kungiyar Moussa Faki Mahamat ya bayyana hakan kwana daya bayan an fitar da wakilin isra’ilan daga dakin taron bude zaman wanda ya gudana a Addis Ababa babban birnin Ethiopia.
Faki ya bawa isra’ilan wannan matsayi a shekarar 2021 wanda hakan ya haddasa rashin amincewa daga kasashen aAfirkan ciki har da Algeria da kuma South Africa.
Wannan tasa shekarar da ta wuce a zaman kungiyar tarayyar Afirkan aka jingine tattaunawa dangane da makomar Isra’ilan aka kuma kafa kwamiti na shugabannin kasashe domin su duba lamarin.
Wannan yake tabbatar da cewa, an jingine matsayin Isra’ilan har sai wannan kwamiti ya fitar da matsaya, saboda hakanan ba’a gayyaci Isra’ila wannan zama ba sa’annan Faki ya tabbatar da cewa ana nan ana bincike dangane da lamarin.
Gwamnatin Isra’ila ta nuna damuwar ta dangane da lamarin wanda ya yada kafafen sadarwa, yadda aka nuno jami’an tsaro na fitar da wakilan Isra’ilan bayan takaddama ta tsawon mintuna.
Gwamnatin Israilan ta zargi wasu kasashe da ta kira da masu tsatstsauran ra’ayi irin su Algeria da South Africa a bayan wannan lamari.
Sai dai South Africa ta musanta wannan zargi inda ta bayyana ce lamarin na Isra’ila matakin da zaman kungiyar ya dauka ne.
Yanzu ba za’a bar Isra’ilan matsayin mai sa ido ba har sai kwamiti ya yanke matsaya dangane da lamarin kamar yadda Clayson Monyela wakili daga South Africa ya bayyanawa kafar yada labarai ta Reuters.
Saboda haka ba lamarin Algeria ko South Africa bane, lamari ne na ka’ida.
A wani labarin na daban kuma Falasdinawa sun yabawa kungiyar Afrika bisa dauka wannan mataki na dakatar da Isra’ilan.