Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, hukumar wasannin kwallon kafa ta Falastinu, ta gode wa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona saboda kin yin wasan sada zumunta da wata kungiyar kwallon kafa ta Isra’ila.
A cikin wani bayani da ya fitar, shugaban hukumar kungiyar kwallon kafa ta Falastinu Jiril Rajub ya bayyana cewa, al’ummar Falastinu sun yi farin ciki da matakin da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta dauka, na kin amincewa ta gudanar da wasan sada zumunci da kungiya da kungiyar kwallon kafa ta Bitar ta yahudawan sahyuniya.
Ya ce wannan mataki ne na jarunta wanda ya cancanci yabo daga dukkanin al’ummar Falastinu da sauran musulmi, da ma dukkanin masu ‘yanci da ‘yan adamtaka a duniya.
Rajabu ya kara da cewa, tun kafin wannan lokacin Barcelona ta sha daukar matakai na nuna goyon bayan ga al’ummar falastinu, da kuma nuna ‘yan adamtaka a cikin lamurra da dama da suke faruwa a duniya.
A jiya ne shugaban kungiyar kwallon kafa ta Bitar Moshe Hugig ya sanar da cewa, Barcelona ta yi watsi da gayyatar da kungiyar kwallon kafan ta yahudawa na neman a buga wasan sada zumunta a tsakaninsu, wanda aka tsara zai gudana a ranar 4 ga watan agusta mai kamawa.
Kasar isra’ila dai itace kasa mafi bakin jini a fadin duniya wanda ake ganin hakan ya sam asali saakamakon kafa asasin kharamtacciyar kasar bisa zalunci gami da kwace.
Dalili na biyu da ake ganin ya janyowa haramtacciyar kasar isra’ilan bakin jini shine yadda sojojin haramtacciyar kasar ta isra’ila suke zaluntar raunana falasdinwa wadanda aka same su a kasar su kuma aka kwace musu gidane ake cigaba da kashe su gami da rauna ta da dama daga cikin su.
Al’ummmi daga fadin duniya kama daga musulmi zuwa wadanda ba musulmi ba dai siuna tpfa albarkacin bakunan su inda suke cigaba da Allah wadari da haramtacciya kasar ta isra’ila.