Wakilan kasashe da dama ne suka taru a Belgrade, babban birnin kasar Serbia a yau, don bikin cika shekaru 60 na kungiyar kasashe ‘yan ba-ruwanmu, wato Non Aligned Movement.
Taron farko na wannan kungiyar da ta gudana a Belgrade a cikin watan Satumban shekarar 1961, ya samu halartar wakilan kasashe 25, ciki har da wadanda suka assasa ta kamar Firaministan India, Jawaharlal Nehru, shugaban Masar Gamal Abdel Nasser, shugaba Sukarno na Indonesia, da Kwame Nkrumah na Ghana, sai Josip Broz Tito na Yugoslavia.
Selakovic ya ce taron bikin cika shekaru 60 da kafuwar kungiyar kasashe ‘yan ba ruwanmu ba shi da wani alkibla ta siyasa duba da cewa babu wata matsaya da za a cimma, ko wata sanarwa da za a fitar, sai dai zai kasance wata hanya da kowa zai nuna ya tuna taron Belgrade na 1961 cikin shauki da alfahari.
Kungiyar ta kasashe ‘yan ba ruwanmu, wadda ta kunshi kasashe 120, da ‘yan kallo 17, ita ce hadaka mafi girma ta kasashe bayan majalisar dinkin duniya.
A wani labarin na daban majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar, Najeriya ce kasar da tafi kin baiwa mata mukaman shugabanci a matakin zabe ko kuma nadi.
Muruli tace yana da muhimmancin matan Najeriya su shiga a dama da su a siyasa, saboda shigar su zai bada damar daukar matakan inganta rayuwar al’umma.
Jami’ar tace da farko dai Najeriya ce ke da wakilai mata mafi karanci a Yankin Afirka dake kudu da sahara da kuma duniya, saboda haka abin takaici ne ga kasar da tafi kowacce a Afirka na rashin baiwa rabin al’ummar ta wakilcin da ya dace.
Muruli tace a zamanin da ake tafiya yanzu da mata suka fi maza yawa, yana da muhimmanci a dinga raba dai dai na mukamai, inda akalla kowanne jinsi zai samu kashi 50.
Shugabar kungiyar mata ta WIPF Ebere Ifendu ta bayyana cewar mazaje sun sace tarin kudin jama’a, saboda haka suke amfani da su lokacin siyasa domin mallake mukaman da ake da su.
Ifendu tace duk da yake basu da kudi, suna da yawan da idan sun hada kan su zasu iya yin tasiri lokacin zaben.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Ifendu na bukatar matan da su kara kokari wajen shiga siyasa a dama da su, maimakon jiran mukamai.