Kungiyar Jihadul-Islami Ta Palasdinu Ta Yi Tir Da Tsokacin Faransa Akan Birnin Quds.
A wani bayani da kungiyar ta Jihadul-Islami ta fitar ta bayyana cewa; Muna yin tir da maganar da ta fito daga bakin Pira ministan Faransa Jean Castex da ya bayyana Quds a matsayin babban birnin HKI na har abada.
Kungiyar ta jihadul-Islami ta kuma kara da cewa; Zance irin wannan yana nuni da halayyar munafinci, da kuma murguda tarihi, sannan kuma a lokaci daya yana ruruta wutar tsattsauran ra’ayi.
Har ila yau kungiyar ta Jihadul-Islami ta ce wannan irin Magana da take fitowa daga bakin jami’an gwamnatin Fransa, babu wani balarabe ko musulmi wanda zai lamunta da ita,domin ta shafi batu mafi muhimmanci a wurin larabawa da musulmi a ko’ina a duniya.
Kungiyar gwagwarmayar ta Palasdinu ta kuma ce; Birnin Quds na larabawa da musulmi ne, kuma na al’ummar Palasdinu ne da yake a matsayin babban birninsu na har abada.