Kungiyar Hizbullah Ta Aike Da Jirgin Leken Asiri Kan Isra’ila Ya Je Ya Dawo Lafiya.
Kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon ta aike da jirgen sama na leken asiri wanda ake sarrafawa daga nesa zuwa kan HKI, ya je ya kuma kammala aikinsa ya dawo ba tare da wata matsala ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana fadar haka a jiya jumma’a ta kuma kara da cewa
“Kungiyar ta aike da jirgen saman leken asiri mai suna ‘Hassan’ zuwa kan HKI, jirgen ya kammala ayyukansa na leken asiri wanda ya dau mintuna 40 yana watayawa kan sararin samaniyar HKI, a lokacinda ya kammala aikin wanda ya kai nisan kilomita 70 cikin kasar ya dawo gida ba tare da ko kwarzane ba.
Labarin ya kara da cewa sojojin Yahudawan sun yi kokarin kakkabo shi amma sun kasa yin hakan har ya kammala aikinsa ya dawo lafiya.
Hukumomin yahudawan sun tabbatar da aukuwan hakan, sun kuma bayyana cewa makaman kakkabo jiragen saman da suka cilla kan jirgen leken asirin sun kasa samunsa har ya kammala aikinsa ya koma cikin kasar Lebanon.