Kungiyar Hamas Ta yi Kira Ga Falasdinawa Da Su Yi Gangami A Masallacin Quds A Gobe Juma’a.
Rahotanni da suka fito daga yankin falasdinu sun nuna cewa kungiyar gwagwamar ta hamas ta yi kira ga dukkan falasdinawa da su yi cincirindo a gobe juma’a a masallacin qudus domin nuna rashin amincewa da mataken zalunci da isra’ila ke dauka.
Masallacin kudus shi ne babban alama ta musulunci da falasdinu amma gwamnatin Isra’ila tana kokarin rusa wannan wuri mai muhummanci sai dai sadaukarwa da tsayin daka da falasdinawa suke nuna ya hana ta aiwatar da mummunan nufinta.
READ MORE : Sojojin Isra’ila Sun Auka Kan Masallata A Cikin Masallacin Quds Da Asubahin Yau.
A gobe jum’aa cewa za’a gudanar da ganganmi domin nuna goyon bayan birnin Qudus da masallacin Qudus da kuma kareshi daga keta huruminsa da isra’aila ke yi , Isra’ila ta mamaye yankin falasdinu ne a shekata ta 19.