Kungiyar EU Tana Nazari Kan Martanin Iran Game Da Batun Farfado Da Yarjejeniyar Nukiliya.
Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da cewa tana nazari kan martanin da Iran ta mayar kan shawarar da ta mika mata kan batun farfado da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015.
Mai magana da yawun jami’in kula da harkokin waje na kungiyar ta EU Josep Borrell, wanda ya jagoranci tattaunawar da nufin daidaita Iran da Amurka yarjejeniyar, ya ce an samu martani daga Iran a yammacin jiya Litinin.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto majiyar tana cewa, “Muna nazarinsa kuma muna tuntubar sauran abokan hadin gwiwa da suke cikin yarjejeniyar, da kuma Amurka kan hanyar da za a bi wajen samun matsayi da dukkanin bangarorin za su amince da shi.
Wasu Jami’an diflomasiyya da manazarta sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa ko da Tehran da Washington suna da wata mahanga ta daban kan shawarar da da kungiyar tarayyar turai ta gabagatar musu domin farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekara ta 2015, da wuya kowanne daga cikinsu ya sanar da yin fatali da shawarar, saboda kiyaye ta zai amfanar da kowannensu.
Amir Abdollahian ya ce, “kwanaki masu zuwa suna da matukar muhimmanci” don ganin ko Amurka za ta nuna sassauci kan batutuwa uku da suka rage.