Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yaƙin da Isra’ila ke yi a kudancin Gaza ya tilasta wa sama da mutum miliyan guda barin gudun hijira daga Rafah.
Rundunar Sojin Isra’ila ta buƙaci farar hula su matsa can gaba da Rafah, kimanin kilomita 20.
Falasɗinawa da dama sun koka kan cewa hare-haren Isra’ila na kashe su a duk inda suka je, inda suke da gararamba ta ko ina a Gaza a ‘yan watannin da suka gabata.
UNRWA ta ce dubban iyalai yanzu haka suna neman mafaka a wuraren da suka lalace da kuma ruguje a cikin birnin Khan Younis, inda hukumar ke samar da muhimman ababen buƙatu na yau da kullum a gare su.
Blinken Ya Kira Jami’an Isra’ila Don Tattaunawa A Kan Batun Yarjeniyar Tsagaita Wuta Ta Gaza
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya kira wasu manyan jami’an Isra’ila domin tattaunawa kan shirin tsagaita wuta a Gaza, in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka.
Blinken ya yi magana da Ministan tawagar yaƙin Benny Gantz da kuma Ministan Tsaro Yoav Gallant, kamar yadda bayanai suka nuna.
DUBA NAN: Jamus Zata Bar Sansanin Sojin Ta Na Nijar A Bude
A duka kiraye-kirayen biyu, ya yaba wa Isra’ila kan wannan shawara, wadda shugaban Amurka Joe Biden ya zayyana, ya kuma ce wajibi ne Hamas ta amince.