Ana ci gaba da gwabza faɗa tsakanin sojojin Isra’ila da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa a gabashin birnin Rafah da ke kudancin Gaza.
Kazalika jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hari kan hedikwatar karamar hukumar da ke kusa da kan iyaka da Masar da kuma gidaje, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka da dama, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Anadolu ya ruwaito.
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas reshen kungiyar Al-Qassam Brigades a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, sun kai hari kan tankar Merkava ta Isra’ila inda suka cinna mata wuta.
Dakarun sun ƙara da cewa sun yi arangama da sojojin Isra’ila da ke cikin wani gini a unguwar Shouka a Rafah.
A wata sanarwa da suka fitar, sun ce sun kai wa sojojin Isra’ila hari da makami mai linzami mai cin gajeren zango na Rajoum da kuma harsasai masu girman gaske.
A wani labarin na daban firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gode wa hukumomin Saudiyya – wacce kasarsa ba ta da wata alakar diflomasiyya da ita – kan “abin kirkin” da suka yi na bai wa wani jirgin kasarsa damar yin saukar gaggawa a Jidda.
“Ina matukar godiya ga wannan karamci na hukumomin Saudiyya ga fasinjojin Isra’ila wadanda jirginsu ya samu matsalar da ta sa har sai da ya yi saukar gaggawa a Jidda,” kamar yadda Netanyahu ya fada a wani gajeren jawabi da ya yi a bidiyo ranar Talata.
Jirgin Saman Kamfanin Air Seychelles, da ke cike da fasinjojin Isra’ila yana kan hanyarsa ne ta zuwa Seychelles daga Tel Aviv.
Tun watan Yulin 2022 Saudiyya ta rufe sararin samaniyarta ta hanyar hana sauka da tashin jirage zuwa Isra’ila.
Jirgin Air Seychelles ya yi saukar gaggawa a ranar Litinin a birnin Jidda na Saudiyya saboda matsalar da ya samu.
A ranar Talata ne kuma ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta ba da wani jirgin ya kwashe ‘yan kasar tata daga Jidda.
A cewar kafar watsa labaran Isra’la, akwai fasinjoji 128 ‘yan Isra’ila a cikin jirgin. An yi maraba da su har ma aka ba su masauki a birnin Jiddan da ke kusa da gabar Tekun Maliya.
Karuwar jita-jita
Duk da cewa Saudiyya ba ta daya daga cikin kasashen yankin Gulf da suka sasanta da Isra’ila a yarjejeniyar sasantawar da Amurka ta tsara, tun lokacin jita-jita ta karu kan batun shiryawar kasashen biyu.
Riyadh da Washington sun sha tattaunawa a kan sharuddan da Saudiyya ta saka na sasantawar, kamar yadda mutanen da suke halartar tattaunawar suka fada.
Amma masu sharhi a Isra’ila na ganin cewa irin wannan yunkurin ya sha cin karo da cikas bayan sanarwar da Isra’ila ta yi na tattaunawa tsakanin ministan harkokin wajenta da takwararsa ta Libiya a birnin Rum.
Sanarwar ta jawo zanga-zanga a Libiya, wacce ta ki amincewa da Isra’ila, lamarin da ya jawo korar Ministar Harkokin Wajen Libiyan Najla Elmangoush.
Amma ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila a ranar Litinin ta yi watsi da batun cewa ita ta fara fitar da zancen tattaunawar ministocin biyu, ba tare da yin wani karin bayani ba.
DUBA NAN: Halin Da Falasdinawa Zasu Shiga Idan Isra’ila Ta Kai Hari Rafah
A cewar mai sharhi Barak Ravid, lamarin ka iya sa wa kasashen Larabawa su sake nesantar sasantawa da isra’ila, kamar yadda ya rubuta a shafin intanet na Isra’ila na Walla.