Saleh al Talib zai shafe shekaru 10 masu zuwa nan gaba a gidan kurkuku idan har an tabbatar da hukuncin da Alkalin kotun ya yi masa.
Alkali ya samu shahararren malamin nan, Sheikh Saleh Al-Talib wanda ya yi limanci a ka’aba da laifi, ya yanke masa hukunci Wata huduba da Al Talib ya yi a shekarun baya, ya soki bukukuwan da aka shigo da su, ya hada shi fada da gwamnatin Saudi.
A ranar Litinin, 23 ga watan Agusta 2022, kotun da aka kafa domin sauraron laifuffuka na musamman ta yanke hukunci ga Saleh al Talib.
Middle East Eye ta fitar da labari cewa an Sheikh Saleh al Talib da laifi, kuma an yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari a Saudi Arabiya.
Kotun daukaka karar ta yi fatali da hukuncin da aka yi a baya, inda aka wanke Sheikh Al Talib wanda tsohon limami ne a masallacin Harami a Makkah.
Kara karanta wannan Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015 Hukumomin kasar Saudi Arabiya sun fara kama Saleh al Talib a 2018, a lokacin ba a bada wani dalili ba.
Ana zargin wata hudubar da ya yi ta jawo kama shi. A wancan lokaci, limamin ya yi Allah waidai da hukumar da gwamnati ta kafa domin kula da nishadi, ya kuma soki bukukuwan da aka shigo da su.
Kungiyar Dawn ta yi Allah-wadai Kungiyar Dawn wanda Marigayi Jamal Khashoggi ya kafa, ta tabbatar da wannan hukunci da aka yankewa Saleh al Talib a shafin Twitter a makon nan.
Abdullah Alaoudh wanda shi ne Kakakin kungiyar ya yi tir da wannan hukunci, yake cewa Mohammed bin Salman ne ke neman rufe bakin malamai.
Gwamnati na kama Malaman Saudi Rahoton yace Talib ya shahara a fadin Duniya, daga wajen Saudi Arabiya, dubban musulmai su na sauraron hudubobi da karatul Al-Kur’aninsa a Youtube.
Kima da martabar babban limamin bai hana a kama shi ba, yayin da Yarima Mohammed bin Salman yake kokarin kawo sauye-sauye a kasar Larabawan. Ba wannan ne na farko ba, kafin yanzu, an ji labari gwamnatin Saudi ta cafke Salman al-Odah.
Jaridar Middle East Monitor tace kwanaki aka yanke hukuncin daurin shekaru 34 a gidan maza ga Salma al-Shehab saboda ya soki gwamnatin Saudi a Twitter.
Source: legithausang