Kotun soji da ta yi zamanta a birnin Buea da ke lardin Kudu maso yammacin kasar Kamaru ta yanke hukuncin kisa kan wasu ‘yan aware masu amfani da Turancin Inigilishi bayan samun su da laifin kai wa wata makaranta hari a watan Okotoban 2020.
To sai dai karkashin dokokin kasar ta Kamaru, wannan hukunci na matsayin na farko ne da ke bai wa mutanen 4 zuwa kotun daukaka kara idan suna bukata cikin kwanaki 30 masu zuwa.
A ranar 24 ga watan Oktoban 2020 ne, ‘yan awaren suka kai hari kan wata makarantar boko ta “Mother Francisca international”, da ke garin Kumba a lardin kudu maso yammacin kasar, inda suka kashe mutane.
A shekarar bara saboda matsalolin da ake ciki na bullar cutar korona, an gudanar da taron ne kai tsaye ta hanyar hotunan bidiyo na yanar gizo, inda masu gabatar da jawabai suka rika gabatar da jawansu da makaloli kai tsaye.
Ya ce har yanzu wanann batu yana daga cikin abin da yke ci wa al’ummomin duniya tuwo a kwarya, a kan haka sun fara tattaunawa kan yadda taron na bana ya kamata ya kasance, duk kuwa da cewa ba a yanke shawara guda kan hakan ba, amma za a ci gaba da tatatunawa domin samun matsaya guda.
Kwatin da ke daukar nauyin shirya tarukan hadin kan musulmi na duniya dai yana karkashin cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya ne, da ke da babban ofishinta a birnin Tehran.
Marigayi Imam Khomenei ne ya kirkiro makon hadin kan musulmi musulmin duniya, wanda ya sanya makon haihuwar manzon Allah a cikin watan watan rabi’ul Awwal ya zama shi ne makon hadin kan musulmi na duniya baki daya.