Kotun ICJ ta umarci Isra’ila da ta dauki matakan magance yunwar da ake fama da ita a Gaza
Yakin da Isra’ila ke yi da Falasdinawa a Gaza – wanda ke cikin kwana na 174 – ya kashe akalla mutane 32,490 tare da raunata 74,889, a daidai lokacin da Firaminista Netanyahu ya ce Falasdinawa za su iya “kaucewa” daga mamayar da za a yi a Rafah.
Kotun ta ICJ ta ce Falasdinawa a Gaza na fuskantar mummunan yanayi na rayuwa kuma yunwa da tsananin rashin abinci na yaduwa.
Kotun ICJ ta umarci Isra’ila da ta dauki matakan magance yunwar da ake fama da ita a Gaza.
Alkalai a kotun kasa da kasa baki dayansu sun bai wa Isra’ila umarnin daukar dukkanin matakan da suka dace kuma masu inganci don tabbatar da isar kayayyakin abinci na yau da kullun ga al’ummar Falasdinu a Gaza.
Kotun ICJ din ta ce Falasdinawa a Gaza na fuskantar mummunan yanayi na rayuwa kuma yunwa da tsananin rashin abinci na yaduwa.
“Kotu ta lura cewa Falasdinawa a Gaza ba barazanar yunwa kawai suke fuskanta ba (…) mummunan fari ma ya kunno kai,” in ji alkalan a cikin umarninsu.
Kasar Afirka ta Kudu ce ta bukaci sabbin matakan a matsayin wani bangare na shari’ar da take ci gaba da yi na zargin Isra’ila da kisan kiyashin da take yi a Gaza.
DUBA NAN: Sin Ta Zama Ta Farko Farko A Zuba Hannun Jarin Waje A Tanzaniya
Kutsen da Isra’ila ke shirin yi ya tayar da hankulan duniya saboda birnin, wanda ke kan iyakar Gaza da Masar yana cunkushe da Falasdinawa sama da miliyan 1.5 a sansanoni da tantuna da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa, wadanda galibinsu suka tsere daga hare-haren da Isra’ila ke kaiwa wasu wurare.