Wadanda suka tsira daga hare-haren ta’addancin birnin Paris din faransa a watan Nuwamban shekarar 2015 sun fara ba da shaida a wata shari’a da aka fara a yau Talata a faransa , inda aka gurfanar da mutane fiye da 10 da ake tuhumar su da aikata ta’addancin.
Hare -haren kunar bakin wake da kuma harbin kan mai uwa da wabi da bindigogi da wasu gungun mahara kashi uku suka kai kan mashaya, gidajen cin abinci da zauren kide-kide na Bataclan da filin wasa da ke birnin Paris wadanda daga baya kungiyar IS ta dauki alhaki ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 130 yayin da kusan 350 suka jikkata.
Cikin watan nan ne Kotun kasar da kebabban birnin faransa watau Paris ta fara sauraron shari’ar mutum guda da ya tsira da ransa cikin maharan da suka kaddamar da farmakin.
Belgium ta mika wa ma’aikatar shara’ar Faransa wani da ake tuhuma da hannu a harin da ‘yan ta’adda suka kai tare da kashe mutane 130 a birnin Paris 2015.
Gwamnatin Faransa ta jadada aniyar ta na yakar ta’adanci tareda daukar matakan zurfafa bincike zuwa wasu daga cikin mutanen da ake sa ran suna da hannu a batutunwan da suka shafi ta’adanci a kasar ta Faransa.
Yanzu haka akwai wasu yan kasashen waje da ake ci gaba da tsare da su bisa laifin ta’adanci.