Wani alkali a wata babbar kotun a amurka ta tabbatar da cewa shugaba Trump yafi kusa da aikata laifin da ake tuhumar sa dashi fiye da ace bai aikata laifin ba, laifin da ake tuhumar Trump dashi dai ya hada da kokarin kautarda majalisar amurka daga tabbatar da shugaba Joe Biden daga zaben daya lashe a zaben nuwamban shekarar 2020.
Alkalin kotun ta gunduma wanda ke zama birnin Los Angeles ya tabbatar da cewa ‘yan majalisa masu binciken laifukan da ake zargin tsohon shugaba Trump suna da ikon binciken sakonnin email din da lauyan Trump ya tura masa a ranar 6 ga watan janairu na shekarar 2021.
Alkalin kotun ya tabbatar da cewa lauyan John Eastman wanda ake zargi da tsara duk yadda za’ad bi domin tabbatarwa majalisar bata tabbatar Jor Biden a matsayin shugaban kasa ba, dole ne ya bada hadin kai kuma ya samar da bayanan da suke a wajen sa domin saukaka ma ‘yan majalisar binciken da sukeyi.
Judge Carter wanda ma’aikacin clinton ne ya tabbatar da cewa laifin da tsohon shugaba Trump ya aikata, na kokarin hana doka aikin ta ne kuma yana dai dai da yunkurin juyin mulki.
”Kamar yadda binciken kotun ya tabbatar yafi kama da ace Trump yayi koarin hargitsa lamarin tabbatar da shugaban kasa ta hanyar da bata daceba, maimakon ace bai aikata ba” kamar yadda alkalin ya tabbatar kuma yace lallai abinda Trump din yayi ya saba wa kowacce irin ka’ida.
Shugaba Trump dai ya musa sakamakon zaben inda ya tabbatarwa da manema labarai cewa an kasa shi a zaben ne sakamakonmagudi inda ya nuna bazai amince da hakan ba kuma zia dauki matakin da yake ganin shine ya dace, ya bayyana sakamakon zaben da aka gudanar a shekarar 2020 wanda ya baiwa Shugaba Joe Biden damar darewa bisa mulkin kasar ta amurka a matsayin mafi girman magudi da aka taba aiwatarwa a tarihin amurkan