Wata kotun tarayyar a Amurka ta tabbatar da laifin wasu ‘yan sanda 3 da suka halarci kamun da ya yi sanadiyar kashe bakar fata George Floyd a 2020 wajen kin taimakawa bakar fatan dan kasar Amruka a lokacin da dan uwansu ya danne masa makogwaro har ya mutu a kan idanunsu.
‘Yan sandan da suka hada da Tou Thao, mai shekaru 36, da Alexander Kueng, mai shekaru 28, sai Thomas Lane, dan shekaru 38, na yi masu shara’a ne a Saint Paul, yan tawayen biranen jihar Minneapolis inda mummunan lamarin ya faru, a yankin arewacin kasar Amruka.
Alkalin kotun ya yanke masu hukumcin ne bayan zaman sauraren shara’ar tsawon kwanaki 2 a karshen shara’ar da ta kwashe tsawon wata guda ana yi
Dan uwan George Floyd, Brandon Williams, ya danganta shara’ar da zama wata yar karamar nasara dake kunshe da dantakaitacen fata, domin an tasarwa kyakyawar alkibla, sai dai ya bayyana cewa duk wannan ba zai taba maido masa ” George”, a duniya ba har abada
Tuni dai kotun taraya ta Minnesota tazartar da hukumcin daurin zaman gidan yari na shekaru 22 da rabi kan dan sanda na 4, Derek Chauvin, bayan tabbatar masa da laifin aikata kisa da gangan sakamakon danne makogwaron George Floyd, da ya yi da guiwar kafa na tsawon mintuna da dama aranar 25 ga watan mayun 2020.