Hukumomin Koriya ta Kudu suna kallon masana’antar halal a matsayin wata dama mai girma da ba za a rasa ba kuma sun ɓullo da tsare-tsare masu yawa don kasancewa a wannan kasuwa mai bunƙasa.
cxcx ffdfdfKamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, wani lamari da ba a zata ya ja hankalin mahalarta taron baje kolin Halal na kasa da kasa na Malaysia da aka gudanar a watan Satumban da ya gabata.
Jami’an rumfar Koriya ta Kudu da ke cikin rumfunan kasashen musulmi irin su Indonesiya da Kuwait, sun ba wa maziyarta shawarar ziyartar kayayyakin halal da ake bayarwa a wannan rumfar, tun daga ciyawa da kayayyakin kiwon lafiya.
Shugaban sashen fitar da abinci a ma’aikatar noma, abinci da yankunan karkara na Koriya ta Kudu Lee Yong-jaek ya shaida wa Al Jazeera cewa “Kasuwar abinci ta halal teku ce mai matukar fa’ida ta bunkasa.”
Bayan da ta zuba jari mai tsoka a duniyar fina-finai da talabijin da kade-kade, a halin yanzu Koriya ta Kudo ta fahimci yuwuwar masana’antar halal ta duniya, wacce ke bayyana rayuwar musulmi kimanin biliyan 1.8 a duniya.
Amma a bisa dabi’a, samar da kayayyakin halal bai dace da kasar Koriya ba, wanda aka kiyasta yawan al’ummar musulmi bai wuce 200,000 ko kasa da kashi 0.4% na al’ummar kasar ba. Koyaya, karuwar buƙatun abinci da abubuwan ciye-ciye na Koriya a kudu maso gabashin Asiya, inda al’adun gargajiyar ƙasar ke da haɓaka, yana ba da dama mai fa’ida ga masu fitar da Koriya.
A shekara ta 2015, shugabar kasar Koriya ta lokacin Park Geun-hye ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da Hadaddiyar Daular Larabawa don inganta kasuwanci a sabbin kasuwanni da suka hada da abincin halal.
A shekarar da ta gabata ne Koriya ta Kudu ta fara fitar da naman sa na Koriya ta Kudu da aka fi sani da hanwoo a karon farko bayan samun izini daga hukumomin kula da harkokin addinin Islama a Malaysia.
Source: IQNAHAUSA