Wasu rahotanni daga Korea ta Arewa sun ce kasar ta yi gwajin wani makami mai linzami da ke cin dogon zango a ranakun karshen mako, gwajin da tuni ya gamu da sukar Amurka bayan da ta bayyana shi a matsayin barazana ga makwabtan Korean da ma kasashen gefe.
Wani masanin makamai da ke sharhi kan sabon gwajin na Korea ta Arewa, ya ce gwajin makamin nan una yadda kasar ta kara karfafa sashenta na fasahar samar da muggan makamai.
Amurka dai ta nanata kargadi kan yadda kasar ke makwabtaka da aminanta da suka kunshi Korea ta kudu da Japan kan ci gaba da fadada bangaren makaman nata wanda ta ce barazana ce ga tsaronsu.
Kamfanin dillancin labaran Korea na KCNA ya ruwaito cewa gwajin ya gudana ne a ranakun asabar da lahadi wanda ke bayyana cewa gwajin makamin ya yi nasara kamar yadda aka tsara.