Kongo; Mutane 19 ne Suka Rasa Rayukansu A Zanga-Zangar Kin Jinin MDD A Kasar.
Jami’an gwamnatin democradiyar Kongo sun bada sanarwan mutuwar mutane akalla 19 a rikicin da ya taso tsakanin jami’an tsaro na MDD da kuma mutane a lardin Kivu ta yamma.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa mutanen wadannan yankuna suna korafin cewa jami’an tsaro na MDD sun kasa karesu daga hare-haren yan tawaye a yankin, don haka suna ganin ba amfanin zamansu a kasar.
A rikicin jiya Laraba jami’an tsaro sun cilla wani abu wanda yay i sanadiyyar faduwar wayoyin wutan lantarki kan masu zanga-zanga wanda kuma ya jawo mutuwar mutane uku.
Labarin ya kara da cewa zanga-zangar kin jinin jami’an tsaron MDD ya yaduwa zuwa wasu yankuna da dama a lardin na Kivu.
READ MORE : Iraqi; Magoya Bayan Muqtada Assadr Sun Mamaye Majalisar Dokoki Don Bayyana Korafinsu.
Sai kuma shugaban rundunar MDD a kasar ya yi allawadai da kissan da aka yiwa jami’an MDD guda uku a rikicin na kwanaki biyu, sannan ya kara jaddada cewa sojojin majalisar suna aiki tare da jami’an tsaro na gwamnatin kongo don samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.
READ MORE : Tattaunawar Makamin Nukilya: Iran Tana Maraba Da Hanyoyin Diflomasiyya.