Wani Tsohon sojan Amurka ya cinna wa kansa wuta a gaban ofishin jakadancin Isra’ila da ke Washington.
Tsohon sojan Amurka din yayi hakan ne don nuna rashin goyon bayansa da kisan kare dangin da isra’ila takeyi palasdinu.
cibiyar yada labaran Falasdinu ta bayar da rahoton cewa, wani jami’in tsaro Tsohon sojan Amurka ya cinna wa kansa wuta a gaban ofishin jakadancin Isra’ila da ke birnin Washington domin nuna rashin goyon bayansa akan kisan kare dangin da isra’ila take akan palasdinawa, da kuma yadda Amurka ke hada baki da gwamnatin sahyoniya wajen aikata laifuka da kisan kiyashi kan Palasdinawa.
Wannan tsohon jami’in na Amurka yana ihu yana cewa: Ba zan zama abokin tarayya a kisan gillar da ake yi wa al’ummar Palastinu ba, yakara da cewa a ‘yantar da Falasdinu.
Kafin ya kai ga kona kansa, ya ce: Kona kansa abu ne mai ban tsoro, amma ba kamar kisan kiyashin da ke faruwa a Gaza ba.
‘Yan sanda da jami’an agajin gaggawa na Washington sun sanar da cewa an kai mutumin asibiti kuma yana cikin mawuyacin hali.
A halin da ake ciki kuma, Ofer Kassif, dan majalisar Knesset (majalisar dokokin sahyoniyawan) a daren Lahadin da ta gabata, ya bayyana cewa firaministan wannan gwamnati, Benyamin Netanyahu, da alama yanada tabin hankali ne, yakuma bukaci kotun kasa da kasa da ta dakatar da yakin Gaza. .
Yayin da yake jaddada cewa Binyamin Netanyahu shine makiyin farko na Isra’ila kuma dole ne a hambarar da shi, ya kara da cewa: Idan yakin Gaza ya tsaya, fursunonin Isra’ila a Gaza za su koma gidajensu lafiya.
Duba nan 👇👇: