Kocin rikon kwarya na Manchester United Ralf Rangnick ya bayyana lallasar da suka sha a hannun Liverpool a matsayin kaskanci.
Tuni Manchester United ta sauko zuwa mataki na 6 a teburin wadda hakan babbar barazana ce a gare ta ta rashin samun gurbi a gasar zakarun Turai.
Manchester United ta yi wasan na jiya ba tare da Cristiano Ronaldo ba, wanda ke cikin jimamin mutuwar dansa, yayin da magoya bayan Liverpool da Manchester United suka yi tarayya wajen karrama dan nasa a minti bakwai da saka wasan na jiya.
Kocin AS Roma Jose Mourinho ya nemi afuwar kungiyar Salernitana, biyo bayan tsokana da kuma bakar maganar da mataimakinsa ya ya fadawa ‘yan kungiyar a ranar lahadin nan.
Bayan wasan ne kuma daya daga cikin masu taimakawa Mourinho wajen horaswa Salvatore Foti yayi tattaki zuwa gaban kocin Salernitana Davide Nicola yana mai fada cewar saura kiris a yi fatali dasu daga gasar Seria A su koma ta B, abinda ya sanya kocin da ya sha kaye kokarin yi wa mataimakin na Mourinho kulli ko dukan tsuguna ka ci doya, inda ka yi gaggawar shiga tsakani.
Yanzu haka dai Salernitana maki 16 kacal gareta bayan buga wasanni 30 a gasar Seria A, abinda ya sa take matsayin ta karshe yayin da ya rage wasanni 8 a karkare kakar wasa ta bana.