Kocin tawagar kwallon kafar Brazil Adenor Leaonardo Bacchi da aka fi sani da Tite ya sanar da shirin yin murabus bayan kammala gasar cin kofin Duniya da za ta gudana a Qatar.
Brazil wadda ta dage kofin Duniya har sau 5 a tarihi a wannan karonma na cikin tawagogin da ake yiwa hasashen yiwuwar su kai labari la’kari da irin rawar da ‘yan wasanta ke takawa a lig lig din Turai.
Cikin kalaman kocin wanda y afara horar da Brazil tun daga shekarar 2016 yana fatan kafa tarihin kawowa kasar kofin duniya na 6.
Brazil dai ta dage kofin duniya ne a shekarun 1958 da 1962 da kuma 1994 kana shekarar 2002, kuma tun daga wancan lokaci ne ta fara fuskantar koma baya a fagen tamaula gabanin zuwansa a 2016 da ya dawo da martabar kasar har ta iya kaiwa wasan gab da na karshe a Rasha yayin gasar cin kofin duniya na 2018 gabanin rashin nasara hannun Belgium da kwallo 2 da 1 wanda ek da nasaba da raunin tauraron kasar wato Neymar Junior.
A wani labarin na daban Da yiwuwar hukumar FIFA ta iya dakatar da ‘yan wasan Brazil da kungiyoyinsu suka gaza basu damar dokawa kasarsu wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Duniya a karshen makon nan.
Zuwa yanzu ‘yan wasan Firimiya 9 Brazil ta sanya a jerin wadanda za su taka mata leda a wasannin neman gurbin, ciki kuwa har da mai tsaron ragar Liverpool Alisson Becker da Fabinho da kuma Firmino, sai ‘yan wasan Manchester City Ederson da kuma Gabriel Jesus kana Thiago Silver na Chelsea da Fred na Manchester United sai Raphinha na Leeds da dan wasan gaba na Everton Richarlison.
Shugaban hadakar kungiyoyin kwallon kafar Turai, Charlie Marshall ya ce kungiyoyin na da sa’o’I 24 don sanin ko za su iya wasannin wannan mako da ‘yan wasansu na Brazil ko akasin haka.
Har zuwa yanzu dai FIFA ba ta sanarwar kungiyoyin yiwuwar dakatar da ‘yan wasan ba idan suka gaza halartar wasan.
Karkashin dokokin yaki da covid-19 dai, matukar ‘yan wasan suka halarci wasannin a Brazil kenan suna bukatar kwanaki 10 idan sun dawo don su killace kansu gabanin fara wasa, wanda ke nuna kungiyoyin za su yi asarar kwanaki fiye da mako biyu ga ‘yan wasan dai dai lokacin da wasannin firimiya suka kankama.
A cewar Marshall a yanayin da ake ciki akwai bukatar FIFA ta tausayawa kungiyoyi wajen basu damar iya hana ‘yan wasan dokawa kasashen wasannin saboda yadda za su rasa damar dokawa kungiyoyinsu wasanni masu muhimmanci.