Kocin tawagar kwallon kafa ta kasar Belgium, Roberto Martinez, ya bayyana rahotannin da ke danganta shi da karbar aikin horas da kungiyar Barcelona a matsayin jita-jita.
Yanzu haka dai Koeman yana fuskantar matsin lamba a Camp Nou sakamakon rashin tabuka abin kirkin Barcelona a sabuwar kakar wasannin da aka shiga, musamman ma bayan kashin da ta sha a hannun Bayern Munich da 3-0 a gasar Zakarun Turai. Wannan ta sa a yanzu haka kocin kasar Belgium Roberto Martinez ya zama daga cikin wadanda ake alakantawa da maye gurbin mai horaswar na Barca.
Sai dai yayin wata ganawa da kafar labarin wasanni ta Eurosport, Martinez ya ce yada jita-jita ba sabon abu bane a fagen wasanni musamman na kwallon kafa, dan haka babu abin da zai ce kan rahotannin da ke yaduwa, domin kuwa babu wata alaka tsakaninsa da shirin horas da Barcelona.
A wani labarin na daban hukumomin Barcelona na duba yiwuwar sallamar mai horar da ‘yan wasan kungiyar, Ronald Koeman, kamar yadda wasu kafofin yada labaran kasar Spain suka ruwaito.
Koeman ya shiga karin matsin lamba ne bayan da Barcelona ta kwashi kashinta a hannu 3-0 a gun Bayern Munich, a wasan farko na gasar zakarun nahiyar Turai da suka gwabza a daren Talata.
Yanzu rahotanni na cewa Ronald Koeman yana da wasani 3 ya ceto kansa daga sallama a kungiyar.
Shugaban Barcelona, Joan Laporta ya ji takaici matuka sakamakon rasin nasarar da kungiyar ta yi a hannun Bayern Munich, kuma gashi a gasar LaLiga za su hadu da Cadiz da Levante.