Manajan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya yi ikirarin cewa har yanzu bai karaya da cewa kungiyar tasa za ta iya dara takwararta Manchester City tare da dage kofin firimiya a bana ba.
A cewar Klopp ya na da kwarin gwiwar cewa Liverpool cikin wannan kaka za ta kafa tarihin dage kofuna 3 ko fiye ciki kuwa har da na firimiya da kuma zakarun Turai da ta samu damar zuwa wasan karshe.
City ta tsawaita tazarar da ke tsakaninta da Liverpool daga maki 1 zuwa 3 bayan lallasa Newcastle da kwallaye 5 da nema wanda ya bata damar zarta ta hatta da yawan kwallaye kwana guda bayan Reds ta yi canjaras da Tottenham da kwallo 1 da 1.
Jurgen Klopp ya bayyana cewa duk da yana fatan shigewa gaban City don lashe kofin firimiya hakan bazai hana shi tattala ‘yan wasansa don tunkarar wasannin karshe na cin kofin FA tsakaninsu da Chelsea a asabar din nan mai zuwa ba da kuma wasan karshe na cin kofin zakarun turai ranar 28 ga wata tsakaninsu da Real Madrid.
A cewar Klopp idan har ba a kai ga wasan karshe ba Liverpool ba za ta cire rai kan yiwuwar dage kofin ba, kalaman da ke zuwa dai dai lokacin da Pep Guardiola na Manchester City ke ikirarin cewa ilahirin Ingila na goyon bayan Liverpool ne don ganin ta lashe firimiya.