Kididdigar baya-bayan nan game da girgizar kasar Turkiyya
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Turkiyya Afad ta sanar da sabbin alkaluman da suka shafi girgizar kasar da aka yi a kasar.
“Anatoliya”, Afad ya sanar da cewa, an kawo karshen ayyukan agaji da ceto a mafi yawan yankunan da girgizar kasar ta shafa a kasar Turkiyya, ban da lardin Hatay da Kahraman Maresh.
Wannan kungiya ta kara da cewa adadin wadanda girgizar kasar ta shafa a Turkiyya ya kai mutane 40,689. “Orhan Tatar”, darektan sashen nazarin girgizar kasa na Afad, ya sanar a wani taron manema labarai a yau cewa ya zuwa yanzu an sami rahoton afkuwar girgizar kasa guda 6,400.
A cewar wannan jami’in na Turkiyya, girgizar kasa 1,628 tsakanin Richter 3 zuwa 4, girgizar kasa 436 tsakanin Richter 4 zuwa 5, girgizar kasa 40 tsakanin Richter 5 zuwa 6 da wata babbar girgizar kasa mai karfin Richter 6.6 ta afku a cikin wannan lokaci.
Girgizar kasa mai karfin maki 7.8 a ma’aunin Richter da ke tsakiyar kasar Turkiyya ta afku a yankuna da dama na yammacin Asiya da kuma Gabashin Bahar Rum da asubahi makonni biyu da suka gabata.
Bayanai daga cibiyoyin binciken girgizar kasa sun nuna cewa, wannan girgizar kasar ta afku a kan iyakar Turkiyya da Siriya da kuma mai tazarar kilomita 26 daga arewa maso gabashin Gaziantep na kasar Turkiyya.
An yi rajistar wannan girgizar kasa a kasashen Turkiyya, Siriya, Lebanon, Falasdinu, Iraqi, Jordan, Masar, Saudiyya da wasu sassan Ukraine da Turai da suka hada da Girka, Bulgaria da…