Khatibzadeh; Yin Tsayin Daka A Gaban ‘Yan Mamaya A Quds Da Falastinu Hakki Ne Halastacce.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatibzadeh ya jaddada cewa, yin tsayin daka a gaban masu wuce gona da iri a kan masallacin Quds da wurare masu tsarki a Falastinu hakki ne halastacce.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar, Khatibzadeh ya yi Allah wadai da hare-haren da yahudawan sahyuniya suke ci gaba da kaiwa kan masallacin Al-Aqsa, da kuma harin da sojojin yahudawan sahyoniya suka kai kan masallata da kuma a wasu wurare masu tsarki, yana mai cewa: Mamaya kan masallacin Al-Aqsa na gaf da gushewa, domin kuwa alumma ta riga ta farka.
Khatibzadeh ya jaddada cewa kulla alaka da gwamnatin yahudawan da wasu kasashen larabawa ke hankoron yi, na daya daga cikin abubuwan da ke baiwa Isra’ila kwarin gwiwa wajen haifar da tashe-tashen hankula da yahudawan suke yi a yankunan Falasdinawa da suka mamaye.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi ishara da karuwar ayyukan wuce gona da iri da matakan da yahudawa masu tsatsauran ra’ayi suke dauka na nuna wariya a yankunan Palastinawa da suka mamaye, yana mai kira ga al’ummomi da gwamnatoci da kungiyoyi na yankin da ma na kasa da kasa, da su mara baya ga al’ummar Palastinu don kare kansu da kuma tinkarar ‘yan mamaya.
Daga karshe Khatibzadeh ya jaddada wajabcin hadin kan kasashen musulmi domin kare Falasdinu da kuma ceto masallacin Al-Aqsa da sauran wurare masu tsarki.