Wata kotu a Pakistan ta wanke tsohon Firaminista Imran Khan daga tuhumar da ake masa da fallasa sirrin gwamnati.
A cikin wani dan takaitaccen hukunci, alkalai biyu na Babbar Kotun Islamabad a ranar Litinin din nan karkashin jagorancin Babban Mai Shari’a Aamer Farooq ya kuma wanke Ministan Harkokin Wajen Khan Shah Mehmood Qureshi, wanda ke da hannu a shari’ar.
Wata kotu ta yanke wa mutanen biyu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari a shari’ar da aka fi sani da “cypher case.”
Lamarin dai na da alaƙa da huldar diflomasiyya tsakanin Washington da Islamabad, wanda Khan ya ce wani bangare ne na maƙarƙashiyar da Amurka ta kulla na hambarar da gwamnatinsa shekaru biyu da suka wuce.
Khan, wanda ya hau kan karagar mulki a shekarar 2018, ya rasa kuri’ar amincewa da majalisar dokokin kasar ne a watan Afrilun 2022, shekara daya da cika wa’adinsa.
Duk da wanke shi, Khan zai ci gaba da zama a gidan yari, bayan da kuma aka yanke masa hukunci a wata shari’ar da ta shafi auren matarsa ta uku, Bushra Khan, wanda ya saɓa wa dokokin Musulunci.
A wani labarin na daban hukumomi a Jihar Neja da ke tsakiyar Nijeriya sun tabbatar da mutuwar gomman mutane sakamakon ruftawar wata mahaƙar ma’adinai a yankin ƙaramar Hukumar Shiroro.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya auku ne ranar Litinin, kuma ya ce mutane da dama sun mutu ko da yake bai bayyana adadinsu ba.
Amma ganau sun ce mutum aƙalla 50 sun mutu yayin da gommai suka jikkata bayan ƙasa ta rufta da su a yayin da suke haƙar ma’adinai a ƙauyen Farin Doki da ke yankin Eran na Shiroro.
Abdullahi Baba Arah ya ce tuni suka kai jami’ansu domin kai ɗaukin gaggawa, yana mai cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata asibitin da ke yankin.
An ƙaddamar da shafin intanet don samun bayanai game da ma’adinai a Nijeriya
“Bayan sa’o’i biyar da ruftawar mahaƙar an samu damar zaƙulo mutane shida da ransu amma suna cikin mawuyacin yanayi,” in ji Abdullahi Yarima, wanda lamarin ya faru a kan idanunsa, kuma tsohon shugaban ƙaramar hukumar