Kenya; Wasu Mambobin Hukumar Zabe Sun Ce An Yi Magudi.
A Kenya Hudu daga cikin mambobin hukumar zaben kasar bakwai sun ki su amince da a fitar da sanarwar sakamakon zaben, suna masu cewa an tafka magudi.
Da take sanar da hakan mataimakiyar shugaban hukumar zaben, daura da takwarorinta, Juliana Cherera, ta ce “Ba za su yarda da sakamakon zaben ba saboda irin magudin da aka tafka a zaben.
Ta ce suna rokon al’ummar kasar da su kwantar da hankalinsu, Akwai damar zuwa kotu kuma shari’ar za ta yi abin da ya dace,” in ji ta.
Da yammacin jiya Litini ne hukumar zaben aksar ta sanar da William Ruto, mataimakin shugaban kasar, a matsayin wanda ya lashe zaben.
William Ruto ya lashe zaben shugaban kasar da kashi 50.49 cikin dari na yawan kuri’un da aka kada, yayin da babban abokin hammayarsa Raila Odinga ya samu kashi 48.8. cikin dari.
Rahotanni sun ce an samu hatsaniyya a cibiyar tattara sakamakon zaben.
READ MORE : Iran, Ta Mika Wa (EU) Matsayarta Game Da Yunkurin Ceto Yarjejeniyar Nukiliya.
An gudanar da zaben ne a ranar Talatar da ta wuce, kuma Wannan ne karo na farko da Mista Ruto mai shekara 55 ya tsaya takarar shugaban kasa.