Kenya Ta Gargadi Facebook Gabanin Babban Zaben Kasar.
Hukumar kula da hadin kan kasa ta Kenya, ta yi barazanar neman rufe shafin facebook, idan kamfanin bai dauki mataki ba game da yada sakwannin nuna kiyaya.
Kwamitin na NCIC, ya baiwa kamfanin na facebook, wa’adin mako guda akan ya bi dokokin kasar game da yayata sakwannin nuna kiyaya, a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da babban zabenta.
Shugaban hukumar, Danvas Makori, ya ce ba zasu bar facebook, ya haifar masu da cikas a harkar tsaro ba, ko kuma ya zama wata hanya ta yada kalamman dake iya tada zamne tsaye ba.
Wani rahoto da gungun Global Witness da Foxglove, suka fitar a ranar Alhamis data gabata ya nuna cewa kamfanin na facebook, ya kasa gano sakwannin nuna kiyaya da ake yadawa a shafin na facebook gabanin zaben na Kenya da za’a gudanar a ranar 9 ga watan Agusta.
Hukumar ta NCIC, ba ta ikon dakatar da facebook, amma tana da hurimin bukatar hakan daga gwamnatin kasar.
READ MORE : Karon Farko, Blinken Da Lavrov, Sun Tattauna Tun Bayan Rikicin Ukraine.
An kafa ta ne bayan rikicin da ya biyo bayan zaben 2007 zuwa 2008, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 1,000 guda.