Kenya; Bangarori Na Kiran A Kai Zuciya Nesa, Gabanin Sanar Da Sakamakon Zabe.
A kasar Kenya yayin da ake shirin sanar da sakamakon babban zaben kasar a cikin sa’o’i masu zuwa, bangarori da dama a kasar na ci gaba da kiran a kai zuciya nesa a kuma kwantar da hankali.
Kungiyoyi masu zaman kansu 14 ne suka hade inda suke kiran ‘yan siyasa da magoya bayan su akan kwantar da hankali yayin da ake shirin fitar da sakamakon zaben.
A gobe Talata ne ya kamata a sanar da sakamakon zaben kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
A ranar Lahadi, hukumar zaben kasar ta ce ta tantance da kuma amincewa da sakamakon zaben data samu daga gundumomi 200 daga cikin 292.
Bayanai daga kasar na cewa an karfafa matakan tsaro ta hanyar jibge jami’an tsaron kwantar da tarzoma da na musamman a gewayen cibiyar kula da tattara sakamakon zaben kasar.
READ MORE : Iran Ta Ce Ba Ta Da Wata Alaka Da Maharin Salman Rushdie.
A halin da ake ciki dai ‘yan takara biyu dake kan gaba a zaben shugaban kasar na ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben.