An gudanar da taron dalibai da masu wa’azi na Tabligi da manyan mutane na wannan kasa ta Kenya tare da halartar dimbin daliban da suka kammala karatun Hauza da kuma masu fafutuka wajen Tabligi da ke aiki a garuruwa da yankuna daban-daban na kasar Kenya.
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) – ABNA – ya habarta cewa, an gudanar da taron dalibai da malaman masu Tabligi da Manyan mutane na kasar Kenya a birnin Nairobi fadar mulkin kasar.
Daliban da suka kammala karatu a makarantar hauza da masu wa’azin Tabligi da yawa da su ke aikin wa’azi a birane da yankuna daban-daban na Kenya sun halarci wannan taron.
A farkon wannan taro, kowane daya daga cikin mahalarta taron ya yi takaitaccen bayani kan ayyukan da suka yi.
A ci gaba da gabatar da taron Hujjatul Islam Walmuslimen, Sheikh Ali Samoja limamin cibiyar Musulunci ta Jafari da ke Nairobi, ya yi tsokaci da cewa: Wajibi ne ya zamo mai Tabligin Addini ya tabbata wajen kara karfafa ilimin wa’azi da fasaharsa domin gudanar da ayyukansa yadda ya kamata domin kara karfafa tasirinsa.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da ci gaban imani da Musulunci da kuma mazhabar Ahlul Baiti (a.s) a nahiyar Afirka, ya ce: Wannan lamari ya kara mana nauyi a cikin ayyukanmu, amma akwai shirye-shiryen ci gaba da gudanar da ayyukan al’adu da addini tare da kara girmama ƙarfin da yaduwar hakan.
Ayatullah Reza Ramezani babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul Baiti (a.s) wanda kuma shi ne babban bako a wajen wannan taro ya yi ishara da cewa akwai gagarumin karbuwar Musulunci a Afirka inda ya ce: zamanin Manzon Allah (SAW) wasu sun kawo uzuri duk da ganin mu’ujiza, amma Bilalul Habashi ba tare da wata mu’ujiza ba bayan ya samu sanin zantuka da koyarwar Manzon Allah (saww) sai ya yi imani da Annabi kuma wannan ruhiyyar abin alfahari ce mutanen Afirka.
Ya ci gaba da cewa: Har yanzu akwai wannan dama mai kyau ga matasa mata da maza na Afirka na koyon addinin Musulunci da koyarwar addini, inda lalle ya zama wajibi a yaba da wannan ruhiyyar.
Babban magatakardar majalisar duniya ta Ahlul-baiti, (AS) ya yi ishara da cewa: Tabbas wajibi ne mu yi taka tsantsan game da tasirin makiya kan tunanin matasa ta hanyoyi daban-daban.
Ya dauki addinin Allah a matsayin mafi girman amanar Ubangiji da Allah ya damka wa malamai da masu Tabligi inda ya ce: yakamata malaman addini su tabbata wajen raya sunan Allah a cikin zukatan mutane.
Ayatullah Ramezani ya ce: Dole ne mu sabunta kanmu bisa ga tambayoyi da bukatun al’umma na wannan zamani da mu ke ciki a yau, musamman matasa, ya kamata mu rika samun damar bitar karatu a kullum.
Ya ci gaba da cewa: Muna da mafi kyawun abubuwan da za mu gabatar wa Al’ummar ‘Yan adam, wanda ya kamata haɗa tarurrukan yawon bude ido da sadarwa fuska da fuska tare da matasa ya zamo cikin shirye-shiryen masu Tabligi.
Source LEADERSHIPHAUSA