Kamar yadda kafar sadarwa ta Aljazeera ta rawaito masu kula da lafiya a yanlin gaza ba su da isassun kayayyakin kula da lafiya
Asibitin Nasser dake Khan Yunus shine babban wurin jinya na karshe a yankin Gaza da Isra’ila ta lalata kayayyakin.
Hukumar lafiya ta duniya tace Isra’ila ta kashe likitoci 627, ma’aikatan jinya, direbobin motar daukar marasa lafiya da sauran ma’aikatan kiwon lafiya tsakanin Oktoba da Janairu.
Tattare da cewa, kusan babu hanyar da kayayyakin za su shiga gaza, baya ga Flasdinawa kusan 2.3 daa aka tilastawa rayuwa cikin yananyi na rashin jin dadi.
Duba Nan: Yadda ‘Yan Sanda Suka Kama Wasu Mutane Kasuwar Magani
A wani labarin na daban, kimanin kasashe 20 ne suka sanar da dakatar da tallafi ga hukumar UNRWA, hukumar dake ba da tallafi ga ‘yan gudun hujirar Falasdinu tun shekarar 1950.
Dalilin dakatarwar a hukumance shine zargn da Isra’ila tayiwa ma’aikatan UNRWA goma biyu da shiga cikin hare haren Hamas a ranar 7 ga Oktoba.
A wani yunkuri na fahimtar da illar dake tattare da rushe UNRWA, musamman a wannan mawuyacin hali da ake ciki mai masaukin baki Dr. Steve Clemons ya tattauna da Leila Hilal tsohuwar mai bada shawara ga kwamishinan UNRWA, da kuma Anne Irfan Malami a Kwalejin jami’ar London kuma marubucin ‘yan gudun hijira kuma tattaunawar ta fayyace batutuwan daya kamata a sani dangane da batun durkusar da hukumar UNRWA wacce ta shafe shekaru tana bada tallafin gaggawa ga falasdinawa masu bukatar taimako.