Mataimakin shugaban Nijeiya, Alhaji Kashim Shettima, ya bayyana shawarar samun ci gaba da tsaro da al’adu da shugaban kasar Sin ya gabatar a matsayin mai albarka. Yana mai cewa kasar Sin ta kasance mai kaunar zaman lafiya da bunkasar arzikin duniya.
Kashim Shettima ya bayyana haka ne yau Juma’a a Beijing, yayin da yake ganawa da wakilan sashen Hausa na CMG a birnin Beijing.
Mataimaki na shugaban Nijeriya, wanda ya zo kasar Sin domin halartar taron shugabannin kasashen Shawarar Ziri Daya da Hanya Daya karo na 3, ya ce karkashin shawarar, kasar Sin ta taimakawa Nijeriya wajen gudanar da manyan ayyukan ci gaba, kamar tashar ruwa mai zurfi ta Lekki da matatar mai ta Dangote da layukan dogo da sauransu, inda ya ce suna neman karin hadin gwiwa da kasar a fannin tabbatar da tsaro da inganta noman rani da sauransu.
Da ya tabo batun huldar Sin da kasashen Afrika kuwa, ya ce, “Sin tana nuna kauna da girmamawa da mutunci da ingantacciyar niyyar alheri ga nahiyar Afrika, kuma ta kan yi hulda da su bisa daidaito da kamanta gaskiya da fahimta da daraja juna, ba kamar wasu kasashe ba.”
Bugu da kari, ya ce, “Nijeriya za ta yi kokarin ganin an kara samun fahimta da lumana a dangantakarsu da Sin domin al’ummar kasar su kara samun ci gaba.” (Fa’iza Mustapha)
Source https://hausa.leadership.ng/abun-da-ya-faru-a-mdd-gargadi-ne-ga-amurka/