Lamarin kashe jami’in DSS na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan da aka kona ofishin hukumar a garin Nnewi na jihar Anambra.
Jaridar ‘Premium Times’ da ake wallafawa a Najeriya ta ce an harbe jami’in mai suna Nwachinaemere Ezemuonye Ozuzu inda hakan yayi sanadiyar kashe shi har lahira a kan hanyar Owerri zuwa Onitsha.
An tura jami’in ne ya gudanar da wani aiki na musamman a jihar Anambra biyo bayan kona ofishin DSS a garin Nnewi, a daidai lokacin da yake komawa.
Babu cikakken bayani a game da lamarin da ya auku, sai dai wata ruwayar na cewa an harbe jami’in DSS din ne bisa kuskure.
A wani labari na daban kuma shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yi alkawarin zurfafa zumunci tsakanin kasarsa da Najeriya, musamman ma ta wajen tinkarar matsalar tsaro.
A cikin sanarwar Macron ya jaddada kudirinsa na yaukaka zumunci tsakanin Faransa da Najeriya, wanda zai kai ga habakar tattalin arziki da bunkasar al’umma.
Shugaban na Faransa ya ce tun bayan da ya ziyarci kasar a shekarar 2018, dangantaka tsakanin Najeriya da Faransa na ci gaba da habaka, musamman ma a fannin tattalin arziki.