Kashe mutum 10 da Isra’ila ta yi a Gaza ya harzuƙa Falasɗinawa.
Fargaba na ƙaruwa bayan luguden wutar da Isra’ila ta yi a kan Birnin Gaza yayin da ‘yan gwagwarmayar Falasɗinawa suka yi mayar da martani da harba makaman roka da tsakar dare.
An harba gomman makaman daga Gaza zuwa cikin Isra’ila bayan dakarunta sun kashe mutum aƙalla 10 yayin hare-hare ta sama da ta kai da yammacin Juma’a.
Jagoran ‘yan gwagwarmayar Falasɗinawa mai suna Tayseer Jabari na cikin waɗanda aka kashe a hare-haren sakamakon abin da Isra’ila ta kira “barazanar gaggawa” da ta fuskanta daga ƙungiyar Palestinian Islamic Jihad (PIJ).
Kazalika, akwai wata yarinya ‘yar shekara biyar da harin ya kashe a Gaza, sannan aka raunata wasu da dama.
PIJ ta mayar da martani ta hanyar harba rokoki fiye da 100 kan Isra’ila cikin dare.
READ MORE : Taiwan: Ziyarar Nansi Pelosi Ta Bar Baya Da Kura A Yankin Asiy.
Sai dai na’urorin tare roka na Isra’ila sun kama da yawa daga cikin makaman da aka harba mata, amma an ji ƙarar jiniya a garuruwan Isra’ila da dama kusan duka tsawon dare.
READ MORE : Amurka ta ce akwai yiwuwar China za ta kai wa Taiwan hari.
READ MORE : Amurka ta sanar da kashe shugaban Al-Qaeda Ayman al-Zawahiri a Afghanistan.