Sojojin Isra’ila sun kuma kashe wani matashin Falasdinu a wani hari da suka kai a kudancin yankin Ya’bad da kuma arewacin birnin west bank a ranar laraba 30 ga watan Nuwamba 2022.
Wanda aka kashe din an tabbatar da cewa matashi ne dan shekara 22 mai suna Mohammad Badarneh, kamar yadda majiyoyin gani da ido suka tabbatar.
Ma’aikatar lafiya ta Falasdin ta tabbatar da cewa an harbi Mohammad Badarneh a kirji da harsasai masu rai, kuma an gaggauta tafiya dashi asibitin Ibn Sina amma kafin a iya bashi taimakonn gaggawa ya riga mu gidan gaskiya.
Kafar yada labarai ta Quds News ta tabbatar da cewa da safiyar ranar larabar dai sojojin Isra’ila sun kai samame garin inda sojojin suka raba gurare kuma suka hau kan rufin gidajen mutane a cikin shirin harbi kowanne lokaci.
Abinda ya biyo bayan hakan shine yamutsi tasakanin mazauna birnin da kuma sojojin Isra’ila masu son tada tarzoma wanda kuma a karshe yayi sanadin kashe matashin da sojojin sukayi.
Birnin west bank dai na fuskantar karin tashe tashen hankula a ‘yan kwanakin nan sakamakonn karuwar hare haren da sojojin Isra’ila ke kaiwa.
A kalla falasdinawa 50 ne suka rasa rayukan su tun farkon wannan shekarar a wasu tarzomomi dake faruwa kamar walkiya tsakanin mutanen gari da sojojin Isra’ila.
Cikin wadanda suka rasa rayukan su a wannan shekarar har da ‘yan jaridar nan mai aiki da kafar sadarwa ta Al-jazeera Shireen Abu Akleh wacce labarin kiasan ta ya shiga lungu da sako na duniya.
A awanni 24 da suka gabata an kashe Falasdinawa shidda a wani sabon salon zaluncin Isra’ila.
Wannan kashe kashe dai na zuwa ne sakamakon sabon salon atisayen da sojojin Isra’ila ke aiwatarwa a arewacin birnin west bank a yankin Jenin da Nablus.
Wannan ta sa yahudawan Isra’ila da suka je Qata kallon kwallon kafan duniyya dake gudana suka bayyana yadda musulmi ke nuna kyamar su gare su.