kasashen Yamma sun fara aikawa Ukraine da tallafin makamai.
Makamai da kayan aiki na kan hanyarsu daga Faransa zuwa Ukraine, yayin da kasashen Yamma ke kai agaji ga Ukraine a yakin da suke da sojojin Rasha da ke ci gaba kutsawa ƙasar.
Shugaba Zelensky ya wallafa a shafinsa na twitter cewa ya yi magana da shugaba Macron na Faransa da sanyin safiyar Asabar.
“Ƙawancen yaƙi da yaƙi na aiki!” kamar yadda Mista Zelensky ya wallafa a shafinsa na Twitter.
A ranar Asabar, Mista Macron ya saka wani bidiyo na kansa yana bayyana cewa: “Yakin zai dore – dole ne mu shirya masa!”