Shugabannin Kasashen Turai sun yanke hukuncin haramta sayen kashi biyu bisa uku na man kasar Rasha sakamakon yadda suka lura lamurra suna kara tsami tsakanin su da rasha, a wani yunkuri na ci gaba da matsin lamba akan tattalin arzikin kasar, yayin da sojojin Rashar ke ci gaba da kai munanan hare hare a Gabashin Donbas dake Ukraine.
Wannan matsayi da shugabannin kasashen na turai suka dauka da zummar hukunta Rasha saboda mamayar kasar Ukraine, zai katse babbar hanyar samun kudaden kasar da ake zargin tana karkata su wajen yakin.
Shugaban majalisar Turai Charles Michel ya bayyana matakin a matsayin tsatsauran mataki akan kasar dan ganin ta kawo karshen yakin.
Shugabannin kasashe 27 dake kungiyar Turai sun shirya taron ne domin cimma yarjejeniya ta dogon lokaci, duk da korafin da kasar Hungary tare da makotan ta ke yi sakamakon dogara da makamashin na Rasha.
Yarjejeniyar shugabannin ta kuma kunshi aikawa Ukraine euro biliyan 9 cikin gaggawa domin inganta harkokin kudaden kasar tare da fitar da babban bankin Rasha na Sberbank daga cikin shirin SWIFT na musayar kudade tsakanin bankunan duniya, tare da haramta ayyukan kafofin yada labaran kasar guda 3 da kuma sanya wasu mutane cikin kundin masu taimakawa wajen aikata laifuffukan yaki.
Kafin cimma wannan matsaya, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana takunkumin cinikin man a matsayin mafi radadi, yayin da ya roki kasashen Turan ad suyi watsi da makamashin Rashar domin samarwa kansu yanci.
A wani labarin na daban ministan Tsaron haramtacciyar kasar Israila Benny Gantz ya ce lokaci ya yi da kasar za ta sanya wasu kungiyoyin Yahudawa biyu masu tsautsauran ra’ayi cikin kungiyoyin ‘Yan ta’adda saboda yadda suke kai hari akan Falasdinawa da kuma kiran kashe Larabawa.
Yayin da yake jagorantar taron jam‘iyyar sa, Gantz yace lokaci yayi da za’a duba yiwuwar sanyawa kungiyar La Familia da Lehave wannan take, kuma ya san ana shirya gabatarwa jami’an tsaro wannan bukata.
Dubban ‘yayan wadannan kungiyoyi ne suka shiga wani tattakin da akayi a karshen mako zuwa tsohuwar Birnin Kudus domin ctuna yadda Yahudawa suka kama Gabashin Birnin Kudus a yakin shekarar 1967.
Daga cikin masu tattakin wasu sun yi ta ambato ‘mutuwa ga Larabawa’, yayin da Falasdinawa suka yi ta musu ruwan duwatsu daga kan kan ginin su.
Firaminista Naftali Bennet ya baiwa ‘Yan Sanda umurnin nuna ba-sani-ba-sabo akan wadanann Yahudawa masu tsatsauran ra’ayi wadanda yace sun shirya tinzira tashin hankali.
Ministan harkokin wajen kasar Yair Lapid ya bayyana kungiyoyin biyu Lehava da La Familia a matsayin abin kunya, wadanda kuma bai dace su dauki tutar Israila ba.
Ita dai kungiyar La Familia magoya bayan kungiyar kwallon kafar Beitar ne wadda tayi kaurin suna wajen nuna wariyar jinsi ga Larabawa da kuma kai musu hari.