Kasashen Turai Na Fama Da Fari Mafi Muni A Shekaru 500 Da Suka Gabata.
Wani rahoto ya bayyana cewa kasashen Turai na fama da fari ko karancin ruwan sama mafi muni a cikin shekaru 500 da suka gabata a nahiyar.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa binciken da wata cibiyay ilmi ta gudanar ya nuna cewa a wannan shekarar ta 2022 nahiyar ta Turai ta rasa kashi 2/3 na ruwan saman da take samu a shekara.
Labarin ya kara da cewa wannan shi ne fari mafi hatsarin da ta fadawa nahiyar a daruruwan shekarun da suka gabata, don haka a wannan shekarar ana fama da karancin ruwa wanda yayi sanadiyyar karancin wutan lantarki da amfanin gona.
Kungiyar tarayyar Turai (EU) ta ce kashi 47% na nahiyar ya tasirantu da karancin ruwan wanda kuma ya shafi yawan abincin da take samarwa a ko wace shekara.
READ MORE : Iran; Kasashen Waje Na Da Hannu A Yaduwar Ayyukan Ta’addanci A Yammacin Asia da Afirca.
Rahoton ya kara da cewa mai yuwa kasashen Turai da kuma wasu yankuna a Asia ta yamma za su yi ta fama da karancin abinci daga cikin watan Augustan mai karewa. Daga karshe rahoton ya kammala da cewa an sami karancin masara da kashi 16% a kakar wannan shekarar 2022 saboda karancin ruwan.