Kasashen Turai Na E3, Sun Fara Bin Isra’ila Game Da Yarjejeniyar Nukiliya.
Iran, ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce sanawar da kasashen faransa, Buritaniya da kuam Jamus, suka fitar, game da tattauanwar neman ceto da yarjejeniyar 2015, ba ta dace ba a yanzu.
Da yake sanar da hakan, Nasser Kanaani, ya ce sam sanarwar kasashen turan ba ta dace ba, sannan ta nuna yadda basu da kyakyawar niyya.
‘’ Abun mamaki ne da nadama, a yadda akayi ta canza yawu da kai kawo tsakanin jami’an diflomatsiyya da kuma mai babban mai jagorantar tattaunawar, kasashen turai su fitar da wannan sanarwa, wacce bata dace ba da kokarin da ake na dage takunkamai.
Ya kuma bukaci kasashen turai da kada su bari masu adawa da cimma yarjejeniya su yi amfani dasu.
M . Kanaani, ya ce, Jamhuriyar Musulinci ta Iran da gaske ta ke domin cimma yarjejeniyar karshe.
Su dai kasashen na faransa, Jamus da kuma Buritaniya, sun bayyana a wata sanarwa da suka fitar a baya baya nan cewa, bukatun da Iran ta gabatar domin farfardo da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da ita a 2015, akwai shakku game da kyakyawar niyyar Tehran domin cimma wata matsaya mai kyau.