Kasashen Musulmi Sun Yi Tir da Hare-haren Da isra’ila Ta Kai Kan Falasdinawa.
Rahotanni sun bayyana cewa Masana da kungiyoyin kare hakki dan adama da dama a kasashen Musulmi sun yi tir da hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan alummar falasdinu musamman a masallacin qudus jiya jumaa kana sun bukaci Alummar duniya da su nuna goyon bayansu ga Alummar falasdinu game da zaluntarsu da isra’ila ke yi.
Dakarun kare juyin musulunci na iran IRGC a cikin wani bayani da suka fitar sun yi tir da mummunan harin da sojojin Isra’ila suka kai kan masallata a masallacin Quds mai tsarki inda suka bayyana hana a matsayin keta hurumin wurin mai tsarki na musulmi
Anata bangaren Cibiyar hadin kan musulmin Africa ta kudu ta yi tir da harin baya bayannan a masallacin Quds a jiyar Juma’a da yayi sanadiyar jikkata mutane 158 bayan da rikici ya barke tsakanin falasdinawa masu zanga-zanga da sojojin Isra’ila.
READ MORE : Matsalar Tsaro; Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP.
Rikicin ya barke ne yan sao’I bayan da sojojin Isra’ila suka kashe wani bafalasdinu a garin jenin dake gabar yammacin kogin Jodan,
READ MORE : Najeriya Za Ta Sayi Jiragen Yaki Daga Kasar Amurka.
READ MORE : Quds; Martani Kan Hare-Haren Isra’ila A Kan Masallacin Aqsa.