Kasashen Musulmi Na Tir Da Kalaman Batancin Da Akayi Wa Annabi Muhammad (saw) A Indiya.
Kasashen musulmi na ci gaba da yin allawadai da kalaman batancin da wata kakakin jam’iya mai mulki a Indiya ta yi kan fiyayen hallita Annabi Muhammad (saw).
Kasashen Iran da Saudiyya duk sun fitar da sanarwowin tir da kalaman na jami’ar da tuni hukunonin indiya suka kore ta.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci jakadan Indiya don nuna rashin amincewa da irin wadanan kalaman na batanci da jami’ar ta yi a wata muhawara da aka yi a gidan talabijin.
A nasa bangaren wakilin na Indiya ya bayyana nadama, kan kalaman da jami’ar ta yi, wadandan ya ce sam basu dace ba kuma gwamnatin Indiya ba zata amince da hakan.
Jakadan ya kuma ce, kalaman da jami’ar jam’iyyar mai mulki, ta yi, basu da wata alaka da gwamnatin Indiya.
Saudiyya ma ta yi Allah-wadai da kalaman da kakakin jam’iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) mai mulki a Indiya, ta yi.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Masarautar ta yi maraba da matakin da jam’iyyar ta BJP ta dauka na dakatar da kakakin.
An dakatar da Nupur Sharma ne a ranar Lahadi sakamakon kalaman batancin da ta yi game da Annabi Muhammad (SAW).
Kasashen Qatar da Kuwait ma duk sun yi tir da kalaman na Sharma.