Kasashen iran da Brazil suna da nisan tsakaninsu da yakai kilo mita 12000 amma dagantakar dake tsake tsakaninsu ta kusanto da su kusa biyo bayan taron da yan kasuwan kasashen biyu suka yi da zimmar kara fadada dangantakar kasuwanci dake tsakaninsu
Jakadun kasahen biyu dukkan su sun amince cewa musayar kudade tsakanin kasashen ta yi kasa sosai , Barazil tana daga cikin manyan abokan huldar kasuwanci na kasar Iran a yankin latin Amurka, huldar kasuwanci dake tsakanin kasashen biyu ta kai tad ala bilina 2.5 a shekara ta 2021 da ta gabata, duk da kalubalen da suke fuskanta na takunkumin Amurka kan iran da kuma Annobar cutar korona virus.
A shekarar da ta gabata cibiyar hadin guiwa ta kasuwanci tsakanin Iran da Brazin ta bude ofishinta a birnin Sao Polo , kuma yanzu haka kasashen biyu suna shirin kara fadada huldarsu a bangaren musayar kudade ta hanyar bankuna, idan shirin ya tafi kamar yadda ake tsara huldar kasuwanci tsakaninsu za ta haura dala biliyan 10 nan da shekara ta 2025