Kasashen Habasha, Masar Da Sudan Suna Tattaunawa A Asirce A UAE.
Wakilan kasashen Masar, Habasha da Sudan suna tattaunawa a asirce a birnin Abudabi na kasar UAE dangane da madatsar ruwa ta renaissance ta kasar Habasha.
Jaridar Sudan tribune ta bayyana cewa kasar Sudan dai tana bukatar kulla yarjejeniya da kasar Habasha kan yadda zata sarrafa ruwan kogin Nilu a madatsar ruwan nata, ta yadda ba zai cutar da kanana madatsun ruwa da take dasu a kan kogin Nilu kasa da na habasha ba.
Sannan kasar Masar tana jin tsaron cewa kasar Habasha tana iya hanata ruwan da take bukata don ayyukanta na noma da bukatun yau da kullum a karshen kogin na Nilu.
A shekara ta 2020 ne gwamnatin kasar Habasha ta fara ciki damatsar ruwan ta renaissance ko GERD.
READ MORE : Najeriya; Jami’an Gwamnati Suna Iya Shiga Harkokin Siyasa Ba tare Da Sun Bar Ayyukansu Ba.
Ya zuwa yanzu dai kasar Habasha ta cika madatsar ruwa har sau biyu, kuma tana bukatar cikata har sau 4 zuwa 7, bukatar ya dangane yawan ruwan da aka samu a ko wace shekara.
Labarin ya kara da cewa tawagogin kasashen biyu sun kunshi kwararru ne a kan al-amuran kogin na Nilu daga kasashen uku. Kuma gwamnatin UAE ce take tsiga tsakani don daidaita kasashen. Mai yuwa idan sun amince kan wani al-amari za a bayyana shi sannan kasashen su rattaba hannu kan yarjejeniya a tsakaninsu dangane da kogin na Nilu.