An bude babban taron Majalisar Dinkin Duniya wanda kasashen duniya da dama ke halarta a China domin nazari game da kare tsirrai da dabbobi da zummar dakile baranazar da suke fuskanta ta bacewa.
Kazalika kasashen duniya da suka hallara, za su tattauna kan zamantakewar halittu da muhalli a taron wanda ke zuwa gabanin babban taron sauyin yanayi na COP26 da zai gudana nan da ‘yan makwanni masu zuwa.
Taron na yau Litinin da ke gudana ta kafar Intanet, zai bai wa bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar Kare Tsirrai da Dabbobi damar tattaunawa kan sabbin dabarun kare muhalli nan da shekara ta 2030.
Daga cikin abubuwan da mahalarta taron za su tafka muhawara a kai, har da wani tsarin kare doran kasa da tekuna da kashi 30 nan da shekara ta 2030, matakin da tuni kasashe da dama suka yi na’am da shi.
Kazalika taron zai yi muhawara kan wani kudiri na takaita amfani da sinadarai a fannin noma da kuma hana kera tarkacen robobi da ke zama shara.
Elizabeth Maruma Mrema, Sakatariyar Majalisar Dinkin Duniya bangaren Kare Halittu da Tsirrai ta ce, dole ne a dauki mataki a cikin shekaru 10 masu zuwa domin dakatar da becewar wasu nau’ukan tsirrai da dabbobi.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da kiyasi ya nuna cewa, kimanin na’ukan dabbobi da tsirrai miliyan guda ne ke fuskantar barazanar bacewa baki daya daga duniya saboda dabi’ar bil’adama wajen lalata muhalli.