Kasashen duniya 200 da suka hadu a taron sauyin yanayi na COP26 a Glasgow na kasar Scotland sun amince da wata yarjejeniya a ranar Asabar don hanzarta yaki da dumamar yanayi, amma ba tare da ba da tabbacin cimma burin rage matakin zuwa 1.5 ° na ma’aunin C ba, haka zalika taron ya Karkare ba tare da amsa bukatar kasashe masu fama da talauci dake nemem dauki ba.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da kansa ya lura da raunin wannan “Yarjejeniyar Glasgow”, yana mai gargadin cewa “har yanzu bala’in yanayi na nan daram”,
A wani labarin na daban an tsawaita taron sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya COP26 dake gudana a Glasgow har zuwa wannan Asabar, bayan da aka gaza cimma matsaya kan matakin karshe na rage gurbatacen iska, inda ranar Juma’a shugaban taron Alok Sharma ya yi kira ga kasashe da su yi kokarin karshe na tabbatar da alkawurran da za su iya shawo kan yanayin zafi da ke barazana ga duniya.
Sharma ya ce yana sa ran za a ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar har zuwa yammacin wannan Asabar yayin da wa’adin ranar 12 ga watan Nuwamba ya wuce ba tare da cimma yarjejeniya ta karshe ba.