Taron majalisar kula da hakkokin bil adama na MDD karo na 48, ya gudanar da wata muhawara a ranekun 14 da 15 ga wata, inda kasashe irin su Venezuela da Korea ta Kudu da Sudan ta kudu da Laos da Sri Lanka da Dominica da Armenia da Maldives da Tanzania da sauran wasu kasashe, suka jinjinawa ci gaban da Sin ta samu a fagen kare hakkokin dan Adam, inda kuma suka bayyana cewa, batutuwan da suka shafi Hong Kong da Xinjiang da Tibet, batutuwa ne na gidan Sin da bai kamata a rika tsoma baki cikinsu ba.
Sudan ta Kudu ta bayyana goyon bayanta ga aiwatar da manufar “kasa daya mai tsarin mulki biyu” a yankin musamman na HK.
Inda ta ce abun jin dadi ne yadda mazauna HK ke more ’yanci da hakkokinsu na bil Adama. Kana ta yi maraba da aiwatar da dokar tsoron kasa a yankin da gwamnatin tsakiya ta yi.
A nata bangaren, Tanzania ta bayyana cewa, girmama cikakken ’yanci da yankunan dukkan kasashe tare da kauracewa tsoma baki cikin harkokinsu na gida, ka’idoji na huldar kasa da kasa.
Kuma Tanzania na adawa da siyasantar da batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam. Haka kuma batutuwan da suka shafi Xinjiang batutuwa ne na cikin gidan Sin da bai kamata a yi musu katsalandan ba.
Har ila yau, Tanzania ta yabawa yadda gwamnatin Sin ke kokarin karewa da daukaka rayuwar jama’arta.
Ta ce Sin ta samu gaggarumar nasara wajen yaki da talauci, inda zuwa karshen 2020, ta fitar da Sinawa miliyan 99 daga kangin talauci. Bugu da kari, ta bada gagarumar gudunmuwa ga aikin yaki da talauci a duniya.