Mali da Nijar da Burkina Faso sun balle daga kungiyar ECOWAS a bara inda suka kafa kawancen kasashen Sahel.
Gamayyar kungiyar kasashen yankin Sahel (AES) da shugabannin sojojin Mali da Nijar da Burkina Faso suka kafa a watan Satumban da ya gabata, ta sanar a yau Lahadi cewa, za ta kaddamar da fasfo na bai daya domin inganta hadin gwiwa da tsaro.
Shugaban kungiyar AES kuma shugaban mulkin sojan kasar Mali Kanar Assimi Goita ya fada a wani jawabi a gidan talabijin cewa nan ba da jimawa ba kungiyar za ta kaddamar da fasfo na bai daya wanda zai kuma saukaka zirga-zirgar ‘yan kasar a fadin kasashen uku.
Ya bayyana hakan ne domin bikin cika shekara guda da kafa kungiyar ta AES tun a ranar 16 ga watan Satumban bara.
Burkina Faso, Mali da Nijar sun kafa kungiyar AES tare da sanar da kafa rundunar soji ta hadin gwiwa domin dakile kalubalen tsaro da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke yi a kasashensu.
Kasashe uku na yammacin Afirka sun fice daga kungiyar ECOWAS, wadda ta yi barazanar shiga tsakani na soji a Nijar, bayan juyin mulkin da aka yi a kasar a watan Yulin bara.
Kasashen uku, wadanda ke da adadin mutane miliyan 72, na fama da matsalar rashin zaman lafiya da kungiyoyin ‘yan bindiga ke haddasawa.
A watan Yulin bana ne dai shugabannin gwamnatocin sojoji uku suka gudanar da taronsu na farko na hadin gwiwa a Yamai babban birnin jamhuriyar Nijar, inda suka sanar da hadakar jihohin Sahel uku.
Da yake karin haske game da “gagarumin nasarori” na hadin gwiwa kan kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin, Goita ya ce AES “a bude take don tattaunawa da abokan hulda na kasa da kasa da kuma abokan huldar yankin.”
Ya kara da cewa, “Wannan hadin gwiwa da aka inganta ya taimaka matuka wajen raunana wadannan kungiyoyin (ta’addanci), don haka ya taimaka wajen inganta tsaro a yankin.
Goita ya ce AES kuma za ta kaddamar da gidan talabijin na kowa.