Akalla kasashe 136 ne suka cimma matsaya na samar ko gindaya haraji bai daya ga manyan kamfanoni masu zaman kan su kamar dai yada hukumar kula da cinikaya dama kasuwanci ta yankin Turai ta sanar a marecen jiya juma’a.
A wani labarin na daban shugaban Amurka Joe Biden da babbar murya ya bayyana cewa cimma wannan matsaya ta karbar haraji bai daya za ta taimaka matuka wajen samar da kuddaden shiga ga kasashen ga baki daya.
Masu bincike dake kasar Amurka na zargin wasu ‘yan kasar Rasha 13 da wasu kamfanoni na Rasha 3 da hannu dumu-dumu wajen katsalandan cikin zaben Amurka da aka yi shekarar data gabata wato 2016.
Rahoton na zargin cewa tun a shekara ta 2014 aka fara kulle-kullen yin kutse cikin zaben na Amurka kafin ma Donald Trump ya bayyana shirinsa na tsayawa takara.