Kasar Yemen Ta Yi Tir Da Zartar Da Hukuncin Kisa Da Saudiyya Ta Yi.
Shugaban ma’aikatar kare hakkin dan’adam a kasar ta Yemen, Ali Dulaimy ya bayyana cewa; Saudiyya ta faki idanun duniya ne da ta shagalta da yakin da ake yi a kasar Ukireniya ta zartar da hukuncin kisa akan mutane da dama.
Dulaimi ya kara da cewa; Abinda ya faru wasa ne da rayukanal’ummar Yemen, don haka muna dora alhakin wannan laifin akan Saudiyya da Amurka.
Shi kuwa Dhaifullahi al-Sahmy wanda ministan ne a gwamnatin Sana’a ya ce; Laifin da Saudiyyar ta tafka akan mutanen Yemen yana da girman gaske,haka nan akan mutanen yankin Qatif.
Har ila yau al-shamy ya ce; Babu yadda za a yi Muhammadu Bin Salman ya tafka laifi mai wannan girma ba tare da yardar iyayengidansa Amurkawa ba, da hakan wani abu ne sananne.”
READ MORE : MDD Ta Bukaci A Dauki Matakan Magance Rikicin Sudan.
Ita kuwa cibiyar da take kula da fursunonin yaki a Yemen, ta ce; Kashe fursunonin yaki na Yemen biyu Hakim al-Budhaini da Hidar al-shuzani da Saudiyyar ta yi, wani lamari ne wanda yake cin karo da dukkanin dokokin kasa da kasa, kuma wani lamari ne ma hatsari.
Ministan na kasar Yemen ya kuma ce; Kisan fursunonin yakin wani abu ne da ba za a taba yin shiru akansa ba.